Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa babban Kodinetan ?ungiyar Manyan Dillalan Fetur na Najeriya (IPMAN), ya yi zargin cewa da ha?in bakin jamian tsaron Najeriya ake ?ibga satar ?anyen mai a kasar nan, can a yankin Neja Delta.
Ya bayyana haka a wata tattaunawa da shi da aka yi a gidan talabijin na Arise TV.
Musa Saidu ya ce duk da irin hanyoyin da?ile yawan satar tulin ?anyen mai da NNPC ya shigo da su, amma abin ba?in ciki wasu jamian tsaro na yi masu ?afar ungulu ta hanyar ha?a baki da ?arayin ?anyen mai ana sakin jiragen ruwan da akan kama da lodin ?anyen mai na sata.
NNPC na bakin ?o?arin ta wajen ganin an da?ile matsalar ?arayin ?anyen mai, amma wasu jamian tsaro ko an kama jiragen ruwa ?auke da ?anyen mai sai su sa a sake su, inji shi.
Ya ce duk da rahoton da suka dam?a wa gwamnatin tarayya, jamian tsaro sun ?i yin komai a kai.
Ya ce rahoton na ?auke sunayen masu hannu dumu-dumu a harkar satar ?anyen mai a yankin Neja Delta.
Daga nan ya buga misali da yadda suka fallasa wani jirgi mai ?auke da ?anyen mai na sata, har sojoji suka kama shi, amma daga baya wani babban soja ya sa aka saki jirgin ruwan.
Ya ce sun bi sawu su na ?orafi har Maaikatar Tsaro ta ?asa, amma maganar kenan.
Sai dai kuma Sojojin Najeriya sun ?aryata wannan zargi da ya yi masu, kamar yadda Kakakin Sojojin Saman Najeriya, Edward Gwabkwet ya yi wa PREMIUM TIMES bayani.

