Site icon Muryar 'Yanci

Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Jarumar Fim

WASU ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun harbe wata jarumar finafinan Nollywood mai suna Ngozi Chiemeke a jiya.

Rahotanni sun ce abin ya faru ne a titin Deeper Life a garin Boji-Boji Owa da ke ?aramar Hukumar Ika North-east ta Jihar Delta.
 Mujallar Fim ta gano cewa an kashe jarumar mai tasowa ne a shagon ta na sana’ar hadahadar ku?i na P.O.S.

Mutanen unguwar sun ce su dai sun ji tashin bindiga a wajajen shagon, to amma kafin su kai ?auki har maharan sun arce daga wurin.

An ?auki gawar Ngozi Chiemeke an kai ta mutuware an aje kafin a yi mata jana’iza.
 Kisan gillar ya haifar da babban ru?ani da ba?in ciki a garin, inda mutane su ka ri?a taruwa gungu-gungu su na tattaunawa a kai. 


 Jami’in ya?a labarai na rundunar ‘yan sanda ta jihar, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da labarin kisan ga ‘yan jarida, ya ce, “Wasu maza da ba a san ko su wanene ba su ne su ka kashe matashiyar matar, amma an fara ?o?arin kama wa?anda su ka aikata wannan abu.”

Mujallar Fim ta fahimci cewa wannan sabon kisan gillar ya faru ne ba da da?ewa ba bayan kisan da aka yi wa Cif Anthony Mkpado, wani ?an kasuwa mamallakin shagon sayar da littattafai mai suna Mkpado Bookshop da ke kallon reshen bankin First Bank a garin na Boji-Boji Owa.

Exit mobile version