Jamian hukumar tsaro ta farin kaya, SSS sun mamaye hedikwatar babban bankin Najeriya, CBN inda suka kwace ofishin gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa a kwai wata ji?a??iya tsakanin jamian SSS da Emefiele kan zargin tallafawa taaddanci.
A baya dai hukumar ta SSS ta nemi kotu ta bata izinin kama Emefiele amma ya fice daga kasar domin hutun shekara da zai kare a gobe 17 ga watan Janairu.
Sai dai a watan Disamba ne babbar kotun birnin tarayya ta haramtawa SSS kama, gayyata, ko kuma tsare Emefiele.
Amma kuma a yau Litinin da jamian SSS da suka isa hedikwatar ta CBN, sun shigo da motoci kusan 20 dauke da jamian tsaro.
Jamian sun kuma hana duk maaikatan bankin shiga ofishin Emefiele.
Peter Afunanya, mai magana da yawun SSS, har bai amsa sakon neman bahasi da wakilin Daily Nigerian ya aike masa ba.

