Soludo yayi takara ne a karkashin inuwar jamiyyar APGA mai mulkin jihar, inda ya kayar da abokan takararsa 18, manya daga cikinsu, Valantine Ozigbo na jamiyyar PDP, da kuma Andy Uba na jamiyyar APC.
Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, Charles Chukwuma Soludo, ya lashe zaben gwamnan jihar Anambara da ke kudu maso gabashin kasar.
Jamiar tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Anambra, Farfesa Florence Obi ce ta ba da sanarwar sakamakon zaben bayan kammala tattara shi da sanyin safiyar Laraba.
Soludo yayi takara ne a karkashin inuwar jamiyyar APGA mai mulkin jihar, inda ya sami kuriu dubu 112 da 229, inda kuma ya kayar da abokan takararsa 18, manya daga cikinsu, Valantine Ozigbo na jamiyyar PDP da ya sami kuriu dubu 53 da 807, da kuma Andy Uba na jamiyyar APC, wanda ya sami kuriu dubu 43 da 285.
Tun a daren Lahadi aka sami tattara sakamakon zaben kananan hukumomin mulki 20 daga cikin 21 na jihar, to sai dai kuma babbar jamiar tattara sakamakon zaben ta bayyana cewa zaben bai kammala ba, har sai da aka sake gudanar da zabe a karamar hukumar Ihiala a ranar Talata.

