Site icon Muryar 'Yanci

Da Dumi-Dumi: Shugaban EFCC Ya Suma A Bainar Jama’a

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati wato EFCC Abdulrashid Bawa ya yanke jiki ya fadi a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

Lamarin ya faru ne lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen wani taro a fadar shugaban kasar.

Kwatsam sai ya daina magana ya yanke jiki ya fadi, daga nan aka yi awon gaba da shi zuwa asibiti.

Wasu manyan mutane ciki har da ministan sadarwar Najeriyar Isah Ali Pantami sun kasance da shi zuwa wani dan lokaci.

Exit mobile version