Bayan kwanaki biyu ana dambarwa kan shugabancin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa, an nada mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa sashin kudu maso yamma Yemi Akinwonmi a matsayin mukadashin shugaba.
Mai magana da yawun jam’iyyar PDP na kasa, Kola Ologbondiyan ne ya sanar da hakan bayan taron sirri da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ta yi a ranar Alhamis a Abuja.
Mr Akinwonmi zai maye gurbin shugaban jam’iyyar na kasa, Uche Secondus, wanda ranar Litinin wata babban kotun jihar Rivers ta hana shi cigaba da zama shugaban PDP na kasa.

