Kotun ?olin tarayya ta ?age sauraron ?arar da wasu gwamnoni suka shigar suna ?alubalantar waadin Babban Bankin Najeriya na amfani da tsofaffin ku?i.
A yanzu kotun ta ce za ta ?age sauraron ?arar har sai ranar uku ga watan Maris, 2023.
Al?alin kotun John Okoro, wanda ke shugabantar shariar ne ya bayyana sabuwar ranar da za a ci gaba da sauraron ?arar bayan ji daga lauyoyin dukkanin ?angarorin biyu.
Tun farko gwamnatin tarayya ta ayyana ranar 31 ga watan Janairun 2023 a matsayin ranar da za a daina amfani da tsofaffin takardun ku?i na naira 1,000, da 500, da kuma 200.
Sai dai daga baya shugaban ?asar Muhammadu Buhari ya amince da ?ara waadin zuwa 10 ga watan Fabarairu.
Amma duk da haka jihohin Kaduna da Zamfara da Kogi sun shigar da ?arar a ranar uku ga watan Fabarairu suna ?alubalantar waadin na gwamnatin tarayya.
Sannan a lokacin zaman kotun na ranar 15 ga watan Fabarairu, wasu jihohin ?asar bakwai sun mara wa jihohi uku na farko baya wurin ?alubalantar matakin na gwamnatin tarayya.
Inda a ranar takwas ga watan Fabarairu ne kotun ta dakatar da gwamnatin tarayya daga aiwatar da waadin amfani da tsofaffin takardun ku?in.

