Babbar Kotun Jihar Kaduna ta sallami Sheikh Ibrahim El-Zakzaky tare da matarsa Zeenat, inda ta wanke su daga dukkan zargin da ake yi musu.
A cewar lauyan Zakzaky, Barista Sadau Garba, kotun ta wanke wa?anda ake zargin daga zargi takwas da gwamnatin Jihar Kaduna ta gabatar mata.
Wakilinmu a Kaduna ya ce jim ka?an bayan bayar da hukuncin ne aka fita da malamin a mota zuwa gida, inda ba su saurari ko ‘yan jarida ba.
“Kotun ta sallame su ne saboda rashin ?wa??warar hujja,” a cewarsa.

