Site icon Muryar 'Yanci

Da Dumi-Dumi: Karuwai Za Su Tsunduma Yajin Aiki A Kaduna

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Kungiyar mata masu zaman kan su (karuwai) reshen Sabon garin Zaria dake jihar Kaduna, sun bayyana aniyar su ta tsunduma yajin aiki biyo bayan kalubalen da suke fuskanta daga maneman su.

Karuwan sun yi Allah wadai da sabuwar dabi’ar da mazaje
suka shigo musu da ita, wadda hakan ta sa suka sanar da cewar akwai yiwuwar su tsunduma yajin aiki na wani lokaci a matsayin jan kunne ga masu nemansu.

Karuwan sun koka kan yadda maneman nasu ke zabtare musu farashi idan sun yi magana sai su ce musu sun kashe kudi da
yawa wajen sufuri saboda karancin man fetir.

Kungiyar ta yi kira ga ‘ya’yan ?ungiyar ta da su kauracewa gidajen shakatawa, otal-otal da duk wajen cin abinci domin tafiya yajin aikin gargadi.

Daga Abdullahi Kolomi Adam

Exit mobile version