Site icon Muryar 'Yanci

Da Dumi-Dumi: Gombe Ya Zama Shugaban Kungiyar ‘Yan Fim

HA?A??IYAR ?ungiyar masu shirya finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta na?a fitaccen jarumi Umar Mohammed Gombe matsayin shugaban ri?o na reshen ta na Jihar Kano.

Na?in nasa ya biyo bayan kafa kwamitin shugabanni na wucin gadi na jihar da ?ungiyar ta yi bayan aje aiki da tsohon shugaban ya yi kwanan baya.

A cikin sanarwar da shugaban Hukumar Amintattu (BoT) na MOPPAN, Alhaji Sani Mu’azu, ya bayar a daren yau, ?ungiyar ta bayyana cewa ta yi haka ne domin ta cike gurbin da rashin kwamitin gudanarwa na ?asa na ?ungiyar ya haifar “a daidai wannan lokaci mai muhimmanci.”

Hukumar Amintattun ta kuma na?a Hajiya Asma’u Sani a matsayin ?aya daga cikin shugabannin ri?on “da nufin a ?ara wa kwamitin wakilcin mata”.

Sauran ‘yan kwamitin su ne: Yaseen Auwal, Saima Mohammed, Kamal S. Al?ali da Sulaiman Edita.

Hukumar Amintattun ta ba ‘yan kwamitin shawarar cewa, “Idan har akwai wani daga cikin su da ya ke da burin tsayawa takarar wani mu?ami a za?en da za a yi, to ya gaggauta aje aiki tun kafin ya bayyana burin sa.”

Ta ?ara da cewa, “BoT ta ?auki reshen Jihar Kano da muhimmanci kamar dai yadda ta ?auki sauran rassan MOPPAN na jihohi, wanda bai kamata a bar shi a baya ba saboda duk wani abu da wani reshe ya aikata, to zai shafi sauran.

“BoT ta yi amanna da cewa kwamitin ri?on zai iya gudanar da za?u??uka a jihar, domin ya na da ?warewa.

“Babban aikin da aka ba kwamitin ri?on na Umar Gombe dai shi ne ya shirya za?en shugabanni na jihar ba tare da wani jan lokaci ba.”

A ?arshe, BoT ta yi kira ga dukkan membobin ?ungiyar da ma dukkan masu ruwa da tsaki a Jihar Kano da su ba sabon kwamitin ri?on ?waryar dukkan goyon baya da ha?in kai da ya ke bu?ata domin ya sauke nauyin da aka ?ora masa.

Exit mobile version