Rahotanni daga ingantattun majiya sun tabbatar da cewa hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ?asa taannati, EFCC, ta tsare uwar gidan gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a Abuja.
A cewar majiyoyin, Hafsat Ganduje, wacce babban ?anta ya shigar da ?orafi a kanta, an gayyace ta don yi mata tambayoyi amma aka tsare ta ranar Litinin da daddare, watakila don ci gaba da binciken ne da safiyar Talata,
Idan za a iya tunawa babban ?an gwamnan jihar Kano, AbdulAzeez Umar Ganduje ne ya yi wa mahaifiyar tasa cune a hukumar EFCC bisa zargin karkatar da wasu ma?udan ku?a?e, daga bisani ya kwashi iyalinsa zuwa ?asar Masar (Egypt).
Mun yi ?o?arin ji daga wasu mu?arraban gwamnan da hukumar EFCC amma hakan ya ci tura har izuwa lokacin ha?a wannan rahoto.

