Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar wasu jamian EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, sun shiga hedikwatar hukumar KASUPDA da ke garin Kaduna inda suka yi babban kamu.
An ruwaito cewa a safiyar Litinin din nan 11 ga watan Oktoba, 2021, aka ga maaikatan EFCC a hukumar KASUPDA, inda suka yi gaba da Darekta Janar na hukumar. Rahotanni sun ce EFCC tayi ram da shugaban hukumar, Malam Ismail Umaru Dikko.
Zuwa yanzu babu wanda ya san laifin da ake zargin Dikko da aikata wa. Wata majiya a maaikatar tace Dikko yana cikin gana wa da maaikatansa ne jamian EFCC su ka shigo ofis, suka ta fi da shi cikin wata motar Toyota Hilux.
An samu yar takaddama tsakanin maaikatan hukumar jihar ta KASUPDA da wadannan jamian EFCC biyu da suka zo dauke da bindigogi a cikin motarsu. Maaikatan KASUPDA sun yi yunkurin hana maaikatan EFCC tafiya da shugaban na su.
Daga baya Malam Dikko ya umarce su da su bude kofa, a tafi da shi. Wannan lamari ya auku ne da kimanin karfe 10:00 na safe. Ana zargin cewa yanzu haka Dikko yana babban ofishin EFCC na shiyyar Arewa maso yamma.
Tun 2019 gwamna Nasir El-Rufai ya nada Malam Ismail Umaru Dikko a matsayin Darekta Janar na KASUPDA. Kafin nan yana cikin masu ba gwamna shawara.
KASUPDA ce hukumar da ke kula da cigaba da tsare-tsaren gine-gine a biranen jihar Kaduna. Wannan hukuma ta yi suna wajen rusa gine-gine a Kaduna.
Rahotanni sun ce tun tuni EFCC ta aika wa Ismail Dikko gayyata, amma ya ki amsa kiransu. Hakan ta sa wannan karo, aka zo aka dauke shi da karfi, da yaji.

