Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya aika da tawaga ta musamman zuwa Sokoto da Katsina sakamakon yadda ?an bindiga ke ci gaba da kai hare-hare a yankunan jihohin.
Mai magana da yawun shugaban Najeriyar Malam Garba Shehu ya sanar da hakan inda ya ce shugaban yana jiran rahoto cikin gaggawa da kuma shawarwari kan matakin da ya kamata a ?auka domin magance matsalolin da jihohin ke fuskanta.
Cikin wa?anda Buharin ya tura akwai babban mai ba shi shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya da Babban Sufeton ?an sandan Najeriya Usman Alkali Baba da daraktan hukumar tsaro ta farin kaya Yusuf Magaji Bichi da daraktan hukumar tattara bayanan sirri ta Najeriya Yusuf Magaji Bichi da kuma shugaban tsaro na rundunar sojin Najeriya Manjo Janar Samuel Adebayo.
Wannan matakin dai na zuwa ne jim ka?an bayan yan ?asar da dama sun nuna ?acin ransu kan kasashe-kashen da ake ?ara samu da garkuwa da mutane a ?asar.
Ko a yau ma sai da wasu yan ?asar suka fita zanga-zanga a wasu sassa na Najeriya har da Abuja babban birnin ?asar.

