Rahotanni daga fadar Shugaban ?asa birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa Legas babban birnin kasuwanci na Najeriya domin ?addamar da wasu ayyuka a yau.
Rahotanni na cewa cikin ayyukan da zai ?addamar har da wasu sabbin jiragen ruwa na ya?i a tashar ruwa ta sojin ruwan ?asar da ke Victoria Island.
Tuni hukumar kiyaye ha?ura ta jihar Legas LASTMA ta ba jama’a shawara da su kiyayi bi ta titin Ahmadu Bello sakamakon ziyarar shugaban.
Tuni sojoji da ?an sanda da jami’an DSS suka cika unguwar Victoria Island wanda nan ne shugaban zai je.
Ana kuma sa ran bayan ?addamar da ayyukan zai halarci ?addamar da wani littafi wanda Chief Bisi Akande ya rubuta.

