Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban ?asa Buhari ta amince da bu?atar Amurka ta mi?a mata ?an sanda DCP Abba Kyari wanda ake zargi da hannu wajen aikata zambar fiye da dala miliyan ?aya ta intanet tare da Ramon Abass.
Ofishin Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya bayyana hakan ranar Alhamis bayan ministan ya gabatar wa Babbar Kotun Tarayya a Abuja bu?atar mi?a ?an sandan wanda tuni aka dakatar da shi don neman amincewarta.
Antoni janar ?in ya ce ya nemi a kai Abba Kyari Amurka ne bayan bu?atar da ?asar ta gabatar masa, inda ya yi amfani da dokar mi?a wanda ake zargi da laifi ?asashen ?etare ta Extradition Act a gaban kotun.
Sai dai babu ?arin bayani a yanzu game da abin da zai faru da sauran zarge-zargen da hukumar ya?i da miyagun ?wayoyi, NDLEA, take yi masa na safarar hodar ibilis idan aka kai shi Amurka.
Tun a 2021 ne Amurka ta zargi DCP Kyari da mu’amala da Ramon Abass, wanda aka fi sani da Hushpuppi wanda kuma tuni yake tsare a ?asar, da damfarar wasu kamfanoni fiye da dala miliyan ?aya.

