Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Majalisar Wakila ta tarayya ta umarci Ministan Sharia Abubakar Malami da ya dakata da goge sashe na 84(12) na Dokar Zabe ta 2022.
Sashe na 84(12) da ke cikin Dokar Zaben dai ya ce dole ne duk wani mai rike da mukamin gwamnati da ke da shaawar yin takara a zaben kasar ya sauka daga mukaminsa.
Sai dai umarnin Majalisar na zuwa ne yayin da ta yanke shawarar daukaka kara kan hukuncin da Kotun Tarayya ta yi na bai wa Ministan umarnin goge sashe na 84(12) na Dokar Zabe ta 2022.
A kan haka ne Majalisar ta nemi ministan shariar kuma antoni janar da ya dakatar da aiwatar da umarnin har sai an kammala daukaka karar.
Ita ma Majalisar Dattawa ta ce za ta daukaka karar bayan sanatoci da dama sun bijiro da bukatar yin hakan a zamansu na ranar Laraba.
Kakakin Majalisa Femi Gbajabiamila ya koka kan dalilin da ya sa aka kai karar kotun da ke Jihar Abiya a Kudancin Najeriya, yana mai cewa majalisa ce kadai ke da ikon sauyawa ko yin doka a KundinTsarin Mulkin Najeriya.
An ruwaito cewa a zaman da ya gudana a zauren Majalisar Dattawa, an samu yar hatsaniya a lokacin da Sanata Sani Musa daga Jihar Neja ya bukaci a cire sunansa daga jerin wadanda suka amince a daukaka karar.
A bayan nan ne dai Gwamnatin Tarayya ta ce jamianta da ke takara ba za su sauka daga mukamansu ba biyo bayan umarnin kotu na soke sashe na 84(12) daga cikin Dokar Zaben.
Mai magana da yawun Ministan Sharia, Dokta Umar Gwandu ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Jumaar makon jiya.
Wannan sanarwar na zuwa ne yan saoi bayan da wata kotu da ke zamanta a Umahia, babban birnin Jihar Abia a Kudu maso Gabashin kasar ta umurci Malami da ya cire sashen ba tare da bata lokaci ba.
Gwandu ya ce matakin da maaikatar shariar ta dauka, biyayya ce ga umarnin da kotu ta bayar.null

