Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Ahmed Halilu a matsayin Manajan-Darakta na kamfanin buga ku?i na ?asa.
Halilu, wanda yayan uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ne, ya ri?e kamfanin a matsayin rikon kwarya bayan murabus din Abbas Masanawa a ranar 16 ga watan Mayu.
An jiyo daga majiya mai ?arfi cewa shugaban ya amince da na?in ne bisa shawarar gwamnan babban banki na kasa, Godwin Emefiele, wanda ke rike da mukamin shugaban hukumar NSPMC.
Halilu na da kwarewa a harkar banki ta sama da shekaru 23, inda ya yi aiki da African International Bank Limited, AIB da Zenith Bank Plc.
Ya halarci kwas na Manyan Ma’aikata karo na 39 a 2017 na cibiyar National Institute for Policy & Strategic Studies Kuru, Jos inda ya samu lambar girma ta na National Institute, mni.
Malam Halilu ya yi digirin farko a fannin Noma B. (Agric), Masters in Business Administration da kuma Masters in International Affairs & Diplomacy duk a Jamiar Ahmadu Bello Zariya.
Har ila yau, mamba ne a Cibiyar Gudanarwa ta Najeriya, NIM.

