Site icon Muryar 'Yanci

Da Dumi-Dumi: An Kona Mai Zagin Annabi Kurmus A Abuja

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wasu fusatattun matasa sun hallaka wani dan kungiyar Bijilante kan zargin kalaman batanci ga Manzon Allah (SAW).

An tattaro cewa an hallaka dan Bijilantin ne a sashen ‘yan Timba dake kasuwar kayan itace a unguwar FHA Lugbe dake garin na Abuja.

Shaidun ganin da ido sun bayyana cewar dan Bijilantin Musulmi ne kuma ya shahara da zagin manzon Allah amma yayi wani sabo a daren jiya washegarin ranar da za a kashe shi.

Bayan kalaman batancin, sai ya gudu ya nemi mafaka a Ofishin yan Bijilanti dake kasuwar misalin karfe 1 na rana.

An tattaro cewa a wannan lokacin fusatattun matasa suka kure masa gudu suka fito da shi karfi da yaji daga cikin ofishin kuma suka kasheshi kai tsaye, daga baya suka konashi.

Wani dan kasuwa a wajen mai suna Halilu yace: “Sunan mutumin Small Hundaru, wannan ba shine karon farko da ya zagi annabi ba.” “An damkeshi yana kokarin sayen abinci a kasuwa da rana, saboda lokacin da yayi batancin, babu mutane sosai a wajen, sai aka buga masa ice a akai. Sai da aka kwace bindigar hannunsa suka lallasa shi kafin hallaka shi.

Exit mobile version