Gamayyar harin sama da sojojin Nijeriya su ka kai ya hallaka wani babban kwamandan ISWAP, Abu Sufyan da maya?an sa da dama a yankin Tafkin Chadi a Jihar Borno.
Jaridar PRNigeria ta jiyo cewa Rundunar Sojin Sama, NAF, a wani ?angare na ‘Operation Hadin Kai’ ce ta kai hare-hare a kan gurin ajiye makaman ISWAP ?in da ke Kusuma da Sigir a ?aramar hukumar Marte a Borno, a ranar Lahadi.
Rundunar ta kai harin ne bayan ta samu bayanan sirri cewa akwai ?an ta’addan a yankin, inda su ke ha?uwa domin su kai hare-hare a yankin da sojoji su ka mamaye.
Wata majiyar sirri ta shaidawa PRNigeria cewa an kai harin ne ta sama ta amfani da jiragen ya?in gwamnati, inda a ka kai mummunan hari kan kayan ya?in ?an ta’addan.
“Bayan nan kuma sauran ?an ta’addan da su ke tserewa a ka tare su a ka hallaka su suma,” in ji majiyar.

