Mai Girma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya kai ziyarar ta’aziya ga Iyalin Marigayi Makaman Karaye Alhaji Musa Saleh Kwankwaso a garin Kwankwaso, inda aka yi addu’ar Allah ya jikansa da rahma ya sa aljanna makomarsa.
A nasa Jawabin Wakilin Hakimin ya nemi Mai Girma Gwamna da ya cigaba da kula da iyalin Makama a matsayin ‘ya’yansa kamar yadda Mahaifinsu shi ma ya dauke shi kamar dansa, sannan ya nemi alfarma da abar wannan sarauta a wannan gida nasu.
A Jwabinsa, Gwamna ya nuna alhininsa bisa rashin Mai Girma Makama inda ya bayyana shi a matsayin mutumin kirki mai hakuri da biyayya. Sannan ya yi alkawarin cigaba da kula da wannan gida duba da amintakar dake tsakaninsa da Marigayin da kuma wakilin Hakimi Baba Musa Kwankwaso.
Gwamna ya samu rakiyar Shugaban masu rinjaye na Majalisa Hon. Alhassan Ado Doguwa, DG Campaign Alh Nasiru Aliko Koki, Shugaban Jamiyyar APC Alh Abdullahi Abbas, Kwamishinoni da masu bawa Gwamna Shawara da Dattijan jam’iyyar APC ta Jihar Kano.
Daga Abubakar Aminu Ibrahim
SSA Social Media, Kano.

