Shugaban ?asa Muhammadu Buhari na jagorantar taron majalisar tsaro a fadarsa ta Aso Villa da ke Abuja, babban birnin ?asar.
Wannan ne karo na uku da Buhari ke ganawa da shugabannin tsaron cikin mako biyu, inda suka yi ganawar ?arshe ranar 4 ga watan Mayu.
Shugabannin tsaron da ke halartar taron sun ha?a da mataimakin shugaban ?asa da hafsoshin tsaro da sakataren gwamnatin tarayya da mai bai wa Buhari shawara kan tsaro da sufeto janar na ‘yan sanda da shugabannin hukumomin sirri da kuma wasu ministoci.
Taron na zuwa ne ?asa da kwana ?aya bayan samun rahoton wani yun?uri da aka yi na haurawa gidan Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ?asa, Ibrahim Gambari, wanda ke kusa da fadar shugaban ?asar.
Rahotanni na cewa an kashe a?alla mutum 80 a fa?in ?asar a makon da ya gabata sakamakon matsalolin tsaro.
A makon nan, ‘yan fashin daji sun sace mutum kusan 40 yayin da suke sallar dare a Jihar Katsina mahaifar shugaban, kodayake an ceto 30 daga baya. Kazalika, sun kashe mutum takwas a Jibiya da ke jihar.
Bugu da ?ari, ‘yan bindiga sun kashe ‘yan sanda biyar da kuma matar ?aya daga cikinsu a Jihar Akwa Ibom da ke kudu maso kudancin ?asar a ?arshen mako.
Za mu kawo muku ?arin bayani da zarar mun samu…

