Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugabannin tsaron da ‘yan Majalisar Dattawa sun shiga cikin wata tattaunawar gaggawa ta sirri.
Hafsoshin tsaron na amsa gayyatar ‘yan majalisar ce domin bayyana musu halin da ake ciki game da ta?ar?arewar tsaro a fa?in ?asar.
Babban Hafsan Tsaro, Manjo Janar Leo Irabor ne ya jagoranci hafsoshin tsaron zuwa majalisar, inda Shugaban Majalisa Ahmad Lawan ya kar?e su.
Sauran jamia’n da ke amsa gayyatar sun ha?a da da shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta NIA da kuma na ‘yan sandan DSS.
Bayan Sanata Ahmad Lawan ya gode musu bisa ayyukan kare tsaron ?asa a madadin majalisar sai suka shiga tattaunawar sirri da misalin ?arfe 11:21.
Muna tafe da ?arin bayani da zarar mun samu.

