Site icon Muryar 'Yanci

Da ?umi-?umi: An Yi Yunkurin Hallaka Sarkin Kano

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Bayero, ya tsallake wani yunkuri na kai masa hari da wani da ba a san ko waye ba ya yi kokarin buge motarsa.

A cewar wani ganau da ya zanta da majiyarmu ya ce lamarin ya faru ne lokacin da Sarkin ke shirin komawa fadarsa kusa da titin Zariya, a cikin Kano.

Tuni dai ‘yan sanda suka cafke wanda ake zargin. Sai dai, ba a bayyana dalilin kai harin ba. Har yanzu ‘yan sanda ba su ba da sanarwar abin da suka gano ba.

Exit mobile version