Gwamnatin jihar Kaduna ?ar?ashin jagorancin Gwamnan jihar Malam Nasiru Ahmad El Rufa’i ta kara daukar ?wa??waran mataki na da?ile bazuwar cutar Corona, bayan sanar da rufe makarantu da wuraren taron biki da gidajen rawa.
A wani sako da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya fitar ya sanar da cewa ma’aikata kasa da mataki na 14 su cigaba da zama a gida da gudanar da ayyukan su a gida har sai abin da hali ya yi.
Kaduna na daga cikin jihohin da aka tabbatar da samun hauhawar alkaluman masu kamuwa da korona a kowacce rana a ‘yan kwanakin nan.
A makon da ya gabata ne muka kawo muku rahotanni a kan wasu jihohi da suka sanar da rufe makarantun firamare da sakandire saboda fargabar dawowar annobar cutar korona a karo na biyu.
Gwamnatin jihar Kaduna ce ta fara fitar da sanarwar cewa ta rufe makarantu kafin daga bisani ta sanar da cewa ta bayar da umarni rufe wuraren taron bikin da gidajen rawar disko.
Gwamnatin jihar Kaduna ta na kira ga mazauna jihar akan su kula tare da kara lura da biyayya ga dukkan matakan kare kai daga kamuwa da yada kwayar cutar korona, yin hakan alhakin kowa da kowa ne.”
A ranar Alhamis ne gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da umarnin rufe dukkan wasu wuraren taron biki, gidajen rawar disko, da cibiyoyin motsa jiki, a wani yunkuri na dakile yaduwar kwayar cutar korona a karo na biyu.
Kazalika, gwamnatin ta takaita harkokin wuraren sayar da abinci; babu zama a ci, sai dai a kunshewa mutum abincinsa ya tafi da shi, duka dai domin ragewa cutar karsashi.

