Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika da yar sa za su gurfana a gaban kotu domin fuskantar tuhuma kan badakalar kwangilar Naira Biliyan 2.7.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta shirya gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, a gaban mai sharia Sylvanus Oriji a babbar kotun babban birnin tarayya Abuja, Maitama, a wannan Alhamis mai zuwa.
An shirya gurfanar da shi a gaban kotu tare da wasu mutane uku: diyarsa, Fatima; Jalal Hamma; da kuma Al-Duraq Investment Ltd, bisa zargin yin amfani da mukaman su ba bisa kaida ba, Wanda adadin Badakalar Ya kai Naira Biliyan 2.7.

