Site icon Muryar 'Yanci

Cin Amanar Kasa: An ?age Shari’ar Babachir Zuwa Watan Oktoba

Wata Babbar Kotu a Abuja ta ?age sauraron shari’ar zargin cin hanci da ake yi wa tsohon Sakataren Gwamnatin Najeriya, Babachir David Lawal, zuwa 6 ga watan Oktoban 2021.

Ana zargin Babachir da aikata laifi 10 da suka ?unshi zamba da ha?a baki wajen karkatar da fiye da naira miliyan 544 mallakar gwamnatin tarayya da aka ware don nome ciyawa a yankin kudu maso gabashin ?asar.

Kamfanin labarai na NAN ya ruwaito cewa hukumar ya?i da rashawa ta EFCC na tuhumar ?anin Babachir mai suna Hamidu da wasu mutum biyu da kuma kamfanoni biyu – Rholavision Engineering Limited da Josmon Technologies Limited.

Kazalika ana zargin Mista Lawal da bai wa kamfanonin kwangila ta hanyar da ba ta dace ba wa?anda yake da hannun jari a cikinsu.

A watan Oktoban 2017 ne Shugaba Buhari ya kori Babachir Lawal daga mu?aminsa bayan wani kwamiti da Mataimakin Shugaban ?asa Yemi Osinbajo ya jagoranta ya bayar da shawarar yin hakan, sannan ya na?a Boss Mustapha a matsayin sabon sakataren gwamnati.

Exit mobile version