Site icon Muryar 'Yanci

Ceto ?aliban ?an?ara: Buhari Ya Taya Iyayen Yara Murna

Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya yi maraba da sakin daliban makarantar kimiyya ta Kankara a jihar Katsina su 340 da ‘yan Bindiga suka arce dasu a ?arshen makon da ya gabata.

mai magana da yawun Shugaban ?asa Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar cikin dare.
“Buhari ya siffanta cetonsu a matsayin babban sauki ga iyayensu, kasar, da kuma duniya gaba daya.”.

A ta?aitaccen jawabin da ya yi bayan sanar da sakin yaran, Buhari ya mika godiyarsa ga dukkan wadanda ke da hannu wajen wannan nasara.
“Gwamna Aminu Bello Masari, da sojoji sun yi matukar kokari. Ina samun labari na tayasu murna. Sojoji sun san aikinsu.

Indai jama’a basu manta ba Mun kawo rahoton cewa an sako daliban makanratar sakandaren kimiya dake Kankara akalla 340 yanzu.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya sanar da hakan a hirarsa da manema labarai a Katsina
“Kawo yanzu, an bamu dalibai 340, daga baya an kara da 4, yanzu akwai dalibai 344 dake hanyarsu ta zuwa Katsina yanzu,” Masari ya bayyana.

Exit mobile version