Site icon Muryar 'Yanci

Burina In Jefar Da Rera Waka In Koma Rera Alkur’ani – Ali Jita

Sanannen Mawa?in finafinan Hausa Ali Isa Jita ya bayyana cewar babban burin da yake dashi a yanzu shi ne jingine wa?a da komawa tilawar Kur’ani.

Mawa?in ya bayyana wannan aniyar tasa ne a tattaunawar da ya yi da sashin Hausa na BBC a shirin daga bakin mai Ita.

Ali Jita ya ?ara da cewar dukkanin wata nasara da Mawa?in zamani ke nema a ?asar Hausa Allah ya bashi, bisa ga haka yana matu?ar godiya da fatan sauya Al?iblar rayuwa a nan gaba.

Sai dai jama’a na cigaba da bayyana ra’ayoyin su kan furucin na Ali Jita, inda wasu ke yi mishi addu’a da fatan cikar burin nasa, yayin da wasu ke ganin shaci fadi kawai ya yi a kalaman nasa.

Exit mobile version