Site icon Muryar 'Yanci

Buhari Zai Sake Barin Najeriya Yau Lahadi

Rahotanni daga Fadar Shugaban Kasa dake babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Abuja a ranar yau Lahadi domin zuwa birnin Accra, Ghana inda zai hallarci taron gaggawa na kungiyar tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS, da za a yi don tattaunawa kan rikicin siyasar kasar Mali.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ne ya sanar da tafiyar shugaban kasar cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, da aka rarraba ga manema labarai a Abuja.

Ana sa ran shugaba Buhari zai dawo gida “a karshen taron na kwana daya.” A cewar Adesina, shugaban kungiyar ECOWAS kuma shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ne ya kira taron.

Kafin kiran taron, Buhari ya gana da jakada na musamman kuma mai sulhu a Mali, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, wanda ya yi masa bayani game da abubuwan da ya tattauna da manyan yan siyasa a Mali.

“A yayin da lamura ke cigaba da sauyawa a Mali, Nijeriya ta yi tir da juyin mulkin da aka yi a ranar 24 ga watan Mayu, da tsare shugaban kasa da firaminista da sojoji suka yi, tana mai kira da cewa a saki dukkan fararen hula da ake tsare da su.”

“Wadanda za su yi wa Shugaba Buhari rakiya sun hada da ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, Ministan tsaro, Bashir Salihi Magashi, Ministan Kasuwanci da Saka Hannun Jari, Otunba Richard Adebayo da Shugaban NIA, Ahmed Rufai Abubakar.”

Exit mobile version