Rahotannin dake shigo mana daga ?asar Saudiyya na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya shafe lokaci yana yi wa alummar kasarsa adduar samun zaman lafiya a Masallacin Kaaba da ke Saudiya, inda ya gudanar da ibadar umarah.
Mai magana da yawun Buhari Garba Shehu ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce, shugaba Buhari da tawagarsa sun yi wa Najeriya da alummarta adduar maido da zaman lafiya da tsaro a kasar da sauran kasashen duniya.
Kazalika shugaban ya yi adduar farfadowar tattalin arzikin Najeriya wanda annobar Korona ta yi wa illa.
Kazalika Shehu ya ce, shugaba Buhari tare da mataimakin gwamnan Madinah, Yarima Saud Al-Faisal sun shafe tsawon lokaci a cikin Masallacin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam, Masallacin da ke zaman a biyu a daraja ga alummar Musulmin duniya.
A ranar Litinin da ta gabata ne, shugaba Buhari ya bar birnin Abuja domin halarttar taron zuna jari karo na biyar da aka gudanar a birnin Riyadh na Saudiya.

