Rahotanni daga Fadar Shugaban Kasa dake babban birnin Tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ?arkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ce ta damu matuka a juyin mulkin da ya faru a ?asar Guinea a ranar Lahadi.
Wata sanarwa daga ma’aikatar harakokin wajen Najeriya ta ce gwamnatin Tarayya ta yi Allah wadai da juyin mulkin tare da bayyana cewa matakin ya sa?awa tsarin dimukuradiyya na ?ungiyar Ecowas.
Sanarwar ta yi kira ga sojojin da suka yi juyin mulkin su gaggauta mutunta kundin tsarin mulki tare da tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

