Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yabawa al ummar jahar Adamawa bisa irin gudumawa da suke bayarwa wajen gina kasa dama wanzar da zaman lafiya a fadin kasa baki daya.
Shugaba Buhari ya baiyana haka ne a lokacinda yake jawabi a fadar mai martaba lamidon Adamawa a ziyaran ta aziya da yakai jahar biyo nayan rasuwar Ahmed Joda.
Shugaba Buhari yace marigayin ya bada muhimmiyar gumawa a lokacin rayuwarsa don haka rashin Ahmed Joda Babban rashine baga jahar Adamawa kawaiba harma da kasa baki daya.
Da wan nan ne ya mika ta aziyarsa ga gwamanatin jahar Adamawa da mai martaba lamidon Adamawa tare da iyalai marigayin dama al ummar jahar tare dayin adu ar Allah madaukakin sarki ya jikansa ya kuma yi masa rahama.
A jawabainsu gwamnanan jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri da mai martaba Lamidon Adamawa Dr Muhammadu Barkinda Aliyu Mustafa sun baiyana farin cikinsu dangane da ziyaran shugaban kasa da ya kawowa jahar ta Adamawa.
Sun kuma baiyana goyon bayansu dangane da ahugabancin Shugaba Buhari indama suka kirayi yan Najeriya da sucigaba da yin adu o i domin nemana taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin kalu balen tsaro a fadin kasan nan baki daya.
Daga bisani dai shugaba Buhari ya wuce zuwa kano domin halartan daurin auren dansa wato Yusuf Buhari.

