Site icon Muryar 'Yanci

Buhari Ya Sabunta Na?in Shugaban Hukumar Za?e

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nada Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, don sake yin shekaru 5 a kan kujerar.

Bayan wa’adin mulkinsa na haramar karewa, shugaban kasar ya sake nada shi. Wasu suna kawo sunayen mutane da dama da suke tunanin shugaban kasa zai nada, ashe ba ta nan gizo ke saka ba.

Idan ba’a manta ba, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya hau kujerar bayan saukar Farfesa Attahiru Jega.

Farfesa Mahmood, kamar yadda aka ga ya tafiyar da zabukan 2019, ya tafiyar da shugabanci cikin adalci da natsuwa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jefa jama’a mamaki bayan kara nada shi Farfesan a wannan kujera, bayan hasashen da ‘yan Najeriya suka yi ta yi akai, ta la’akari da girma da matsayin wannan kujerar.

Exit mobile version