Tsohon gwamnan Jihar Borno da ke Alhaji Ali Modu Sheriff, ya ce ya janye daga takarar neman shugabancin jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Modu Sheriff ya fa?a wa BBC Hausa cewa ya janye takarar ce saboda biyayya ga Shugaban ?asa Muhammadu Buhari.
“Shugaban ?asa na son shugaban jam’iyya ya fito daga Arewa ta Tsakiya. Shugabanmu ne, babanmu ne, duk abin da yake so shi za mu yi. Ni ba na jayayya da iyayena a kowane fanni,” in ji shi.
Matakin tsohon gwamnan na zuwa ne bayan jam’iyyar ta ce ta ware wa shiyyar arewa ta tsakiya mu?amin shugaba na ?asa yayin ganawar da gwamnoninta suka yi da Shugaba Buhari a watan Fabarairu.
An ware wa shiyyoyin Arewa mu?aman da na Kudu suka ri?e a cikin shekara takwas da suka wuce, su ma na Kudu haka, a cewar Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai.
Bisa wannan tsari ne jam’iyyar za ta za?i ssabbin shugabanninta a babban taron da za ta gudanar ranar 26 ga watan Maris.
Ali Modu Sharif ya gode wa dukkan mutanen da suka goya masa baya”, amma ya ce ba zai daina siyasa ba.
“Ina jira daga nan zuwa Juma’a, idan jam’iyya ta ce kowane yanki zai iya tsayawa takara ina nan,” a cewarsa.
Da aka tambaye shi ko zai bar siyasa, sai ya amsa da cewa: “Ba zan bar siyasa ba. Don me zan bar siyasa?
“Ba zan nemi wani mu?ami ba sai na shugaban jam’iyya saboda na taimaka wa jam’iyyarmu mai girma.”

