Site icon Muryar 'Yanci

Buhari Ya Lashe Kyautar Gwarzon Shugaba Na Shekarar 2021 A Afrika

Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya lashe kyautar gwarzon gina hanyoyi na shekarar 2021, Shugaban zai amshi kyautar ne daga hannun takwaransa na ?asar Egypt, Abdul-Fattah Al-Sisi wanda ya lashe shekarar data gabata.

Za’a mi?a kyautar ga wanda ya samu nasara a taron shekara-shekara na bankin AfDB ranar 24 ga watan Yuni, An bayyana shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe lambar yabon “Gwarzon mai gina hanyoyi 2021′ wacce akewa la?abi da Trophée Babacar Ndiaye, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Shugaban ?asar Najeriya ya ?wace kyautar ne daga hannun shugaban ?asar Egypt, Abdul Fatta Al-sisi wanda ya lashe kyautar a shekarar 2020.

A jawabin da bankin Africa AfDB ya fitar jiya, yace an bayyana sunan Buhari a matsayin wanda ya lashe kyautar a wajen bu?e taron masu gina hanyoyi ranar 31 ga watan Maris a Cairo, Egypt.

An ?ir?iri wannan kyautar ne domin nuna girmmawa ga shugaban AfDB, Babacar Ndiaye, daga 1985 zuwa 1995.

Exit mobile version