Site icon Muryar 'Yanci

Buhari Ya Gaza Wajen Biyan Soyayyar Da ‘Yan Najeriya Suka Gwada Mishi – Ramadan Gwale

Tsantsar soyayyar da ‘yan Nijeriya suka nunawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan zabensa da suka yi sau biyu, ita ce lokacin da ba shi da lafiya ya kwanta a asibiti a Landan sama da kwana dari. Ko Ina, Masallatai da Coci, ko Ina sai kaji ana cewa ayiwa Shugaban kasa adduah Allah ya bashi lafiya.

Bil hakki muka dinga yiwa Shugaban kasa addu’a akan Allah ya bashi lafiya. Na san har a cikin Sujjada ina yi wa Shugaban kasa addu’ar samun sauki a lokacin, haka kuma, miliyoyin mutane haka nan suke yi masa addu’a a kebantattun lokutan da suka san Allah yana amsa addu’a.

Duk irin wannan nuna soyayya da kauna da muka nunawa Shugaban kasa, bai biyamu ba har yanzu. Allah ya sani ba mun yi bane dan ya biyamu din, abinda kawai muke nema a wajensa shi ne “Shugabanci Nagari Mai cike da adalci.” Amma aka wayi gari ana kisan mutane Babu kakkautawa a Arewa, abinda Shugaban kasa yake yi iya yi kawai shi ne ayace “Bai ji Dadi ba,” ko yace “Allahwadai.” Bai taba cewa ya kasa bacci saboda kashe kashen da ake yi ba.

Babban abinda ya bani mamaki kuma ya daure min kai, shi ne, ace an yi irin wannan ta’annati a garin KANKARA na sace dalibai, Shugaban kasa yana Daura, Amma sai naji ance wai ga wata kakkarfar tawaga daga Abuja tazo Katsina ta gana da Gwamna dan jajanta masa abinda ya faru, ikon Allah, Shugaban kasa kuma yana Daura ana Dama masa Fura da Kindirmo yana sha yana Allahwadai.

Mun kyautatawa Shugaban kasa zato cewar, bilhakki yazo yayi shugabanci na gaskiya da adalci, to Amma gaskiyar lamari ya kasa gano bakin zaren matsalolin kasarnan, an bashi dukkan Uzurin da ya kamata, duk kuwa da cewar, dukkan zarge zargen da ya yiwa shugabannin da suka gabata akan basu iya Shugabanci ba, yanzu ta tabbata sun fishi iyawa. Domin a yanzu rayuwa tafi tsananta ga Talakawa sama da lokacin da ya shude.

Shugabancin Nan dai nauyi ne, Kuma kamar yadda Malamai suke cewa, Nadama ne da Danasani a cikinsa ranar gobe kiyama, Ina jiyewa Shugaban kasa tsoron yafi dukkan shugabannin da suka gabace shi Nadamar wannan Shugabancin da yake na kin bin shawarwarin mafiya rinjayen ‘yan Najeriya, Allah ya kiyaye.

Shekarun da suka rage masa a wannan Mulkin basu wuce uku ba, matsaloli kullum karuwa suke, ba a warware na baya ba, balle a tunkari sabbi, kuma bai taba nuna cewa ya gaza ba, ai masa uzuri, Dan Haka zamu cigaba da kalubalantarsa har sai ya gane gaskiyar halin da ‘yan Najeriya na kasa suke ciki ya gyara. Allah ka bashi ikon gyarawa in yana da niyya, Muna kuma rokonSa da ya yi mana canji mafi alheri. Amin.

Exit mobile version