Gwamnatin tarayya ?ar?ashin jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta fitar da Naira biliyan 11.82 da nufin a biya tsofaffin maaikata hakkokin da su ke bi a karkashin tsarin fansho na CPS.
An ruwaito cewa za a biya tsofaffin maaikatu da su ka yi aiki a hukumomi da maaikatun gwamnatin tarayya shekarun da suka wuce gaba daya ba tare da wani jinkiri ba.
Babban jamiin hukumar kula da fansho na kasa ta PenCom, Peter Aghahowa, ya bayyana wannan a ranar Laraba, 6 ga watan Junairu a yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a birnin tarayya.
Mista Peter Aghahowa ya ce kudin da aka fitar ya kunshi hakkokin maaikatan da su kayi wa gwamnati aiki har zuwa watan Yunin 2004.
Aghahowa yake cewa a wannan lokaci ne gwamnati ta shigo da dokar fansho na kasa a Najeriya.
Jawabin ya ce: Hukumar (PenCom) ta yaba da kokarin gwamnatin tarayya na ganin an fito da hakkokin tsofaffin maaikata, za a biya su. Mun godewa tsofaffin maaikatan gwamnatin da abin da ya shafa da su kayi hakuri. Inji sa.
Idan za ku tuna a watan Agustan shekarar 2020, gwamnatin tarayya ta bukaci a ware N14.92 da nufin a biya wasu tsofaffin maaikatan kasar.
Hukumar PenCom ta bayyana cewa za a yi amfani da kudin da aka ware ne wajen biyan tsofaffin maaikatan kasar bashin kudinsu na watanni hudu.

