Shugaban kasa Muhammadu Buhari na son ya sake ranto dala biliyan 6.1 daga ?ungiyoyin ?asar waje domin cike gi?in kasafin ku?i na 2021.
Jumillar ku?in a naira sun kai tiriliyan N2.343 – kan canjin N379 a kowace dala.
Cikin wata wasi?a da ya aike wa majalisun tarayyar ?asar a ranar Talata, Buhari ya nemi amincewarsu domin kar?o wani sabon bashin.
Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Idris Wase, shi ne ya karanta wasi?ar a zauren majalisar, yayin da Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ya karanta a tasu majalisar.
Kasafin ku?in na 2021 ya nuna cewa za a samu gi?in naira tiriliyan biyar daga cikin jumillar tiriliyan 13.6.

