Site icon Muryar 'Yanci

Buhari Estate Mallakar ‘Yan Sanda Ne Ba ‘Yan Bindiga Ba – ‘Yan Sanda

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa ‘yan bindiga sun mamaye wani rukunin gidaje mai suna Buhari Estate da ta mallaka a yankin Badagry na Jihar Legas.

Cikin sanawar da fitar a ranar Asabar, rundunar ta ce wani mutum ne “da ya yi kama da mai ilimi wanda ya kamata a ce ya san ha?arin ya?a labaran ?arya yake ya?a bayanai da zimmar tayar da fitina” a wani bidiyo, yana i?irarin cewa ‘yan bindiga ne suka mamaye rukunin gidajen.

Sanarwar ta ce rukunin gidajen mallakin rundunar ne kuma jami’an ‘yan sanda ne da iyalansu suka mallake su ta hanyar wani shirinta.

“Rundunar ‘yan sanda na shawartar mutane kan muhimmancin tantance abu kafin ya?a shi don kauce wa tashin hankali, musamman idan aka yi la’akari da mabambantan ?abilun da ke cikin ?asa Najeriya.

Exit mobile version