Labarin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai ba kowa umurnin kara farashin man fetur ta hanyar cire tallafin gwamnati ba.
Ahmad Lawan ya bayyana hakan ne yayin hirarsa da manema labarai bayan ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa ranar Talata, 18 ga Junairu, 2022.
Yace yana farin cikin fadawa yan Najeriya cewa Buhari bai sa kowa cire tallafin mai ba, wasu ne suka yi haka bai da hannu a ciki.
“Ina son yan Najeriya su san abinda nazo tattaunawa da Shugaban kasa.” “Da yawa cikinmu mun damu da maganganu, zanga-zanga, da jama’ar mazabunmu ke yi na cewa gwamnatin tarayya zata cire tallafin man fetur.” “Ina farin cikin sanarwa yan Najeriya cewa shugaban kasa bai fadawa kowa a cire tallafin man fetur ba.”
Idan ba a manta ba bayan fitowar labarin ?arin farashin mai din Kungiyar Kwadago ta ?asa NLC, ta lashi takobin cewa yan Najeriya ba zasu yarda da wani sabon karin farashin man fetur da sunan cire tallafin mai.
NLC ta yi kira ga ma’aikata da yan Najeriya su shirya zanga-zanga kan wannan abu da gwamnati ke shirin yi. Shugaban NLC, Ayuba Wabbab, ya bayyana hakan a jawabin shiga sabuwar shekara da ya saki ranar Asabar.

