Tsohon dan majalisa daga jihar Kano a Jamhuriya ta biyu, Dattijo Dakta Junaidu Mohammed ya ce ba za’a taba samun zaman lafiya a Najeriya ba matukar shugaba Buhari da APC suna kan mulki.
A cewarsa, batun gyaran Najeriya fa ya fi karfin karfin shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Dakta Junaid ya bayyana hakan ne yayin da yake martani a kan kisan manoma 43 da mayakan Boko Haram suka yi wa yankan rago a ranar Asabar.
“Na san ya zuwa yanzu ‘yan Najeriya sun gaji da labaran kisan fararen hula a yankin arewa maso gabas, musamman a jihar Borno da sauran sashin Arewa.
“Yanzu kuma babu sauran dan Najeriya da bai yarda cewa akwai ‘yan bindiga da ke kashe mutane a arewa maso yamma, musamman jihar Zamfara, Katsina, Sokoto, da Kaduna ba. “To babu amfani a wurin wannan lusarar gwamnati ta ke aika sakon jaje duk lokacin da ‘yan ta’adda suka kashe mutane, ya kamata a ce an wuce wurin da zasu rin?a fitowa suna cewa kisan fararen hula ya girgizasu.
“Duk abin da ya ke faruwa, ya na faruwa ne saboda babu gwamnati a kasar nan.
“Matukar dai Buhari da APC za su cigaba da zama a gwamnati, ba za’a taba samun zaman lafiya a Najeriya ba, mulkin Najeriya ya fi karfinsa, ba zai iya ba. “Ya fadi kasa warwas, amma saboda munfurci irin na ‘yan Najeriya, da kabilanci, da nuna bangaranci, da siyasar addini, wasu gani suke Buhari ya na tabuka wani kirki.
“Bai tabuka komai ba Kuma babu abinda zai iya yi, idan ‘yan Najeriya suna son ganin canji sai su yi wani abu ko kuma su yi shiru, su daina korafi,” a cewar Dakta Junaid.

