Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum ya haramta raba abinci ga dubban ?an gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu.
Manufar matakin shi ne domin taimaka masu yin dogaro da kai. Sai dai wasu na ganin matakin zai ?ara haifar da matsalar ?arancin abinci mai gina jiki.
Gwamnatin Borno ta da?e tana son rufe sansanonin ?an gudun hijira domin mayar da su garuruwansu.
Gwamnan yanzu ya haramta wa ?ungiyoyin agaji raba abinci ga wa?anda suka samu matsuguni domin su yi dogaro da kansu.
Yankin arewa maso gabashin Najeriya na fuskantar barazanar ?arancin abinci saboda har yanzu yin noma na da hatsari. Wasu ?ungiyoyi agaji sun ce taimakon har yanzu yana da amfani.

