Site icon Muryar 'Yanci

Borno: Za Mu Rufe Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira Nan Da Wata Biyu – Zulum

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Gwamnatin Jihar ta sanar da shirinta na rufe dukkan sansanonin ‘yan gudun hijira da ke ?waryar Maiduguri, babban birnin jihar nan da ?arshen watan Disamba.

Gwamna Babagana Umara Zulum ne ya sanar da hakan yayin da yake zantawa da ‘yan jaridar fadar gwamnati bayan ganawarsa da Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ranar Juma’a.

Ya ce sun ?auki matakin ne sakamakon ci gaban da aka samu a harkar tsaro da kuma aikin mayar da ‘yan gudun hijirar garuruwansu na asali.

“Na zo ne na yi wa shugaban ?asa bayani game da ?o?arin da gwamnatin Borno ke yi wajen mayar da ‘yan gudun hijira garuruwansu,” a cewarsa.

“Zuwa yanzu komai yana tafiya daidai, gwamnatin Borno ta gama tsara yadda za a tabbatar an kulle dukkan sansanonin ‘yan gudun hijira da ke cikin Maiduguri kafin 31 ga watan Disamba.”

Exit mobile version