Gwamnatin Jihar Borno ta amince da kashe Naira miliyan 88.5 don horaswa da kuma horar da maaikatan gwamnati 1,050.
Shugaban Maaikatan jihar Barista Simon Malgwi, ya fadi hakan a Sakatariyar Musa Usman da ke Maiduguri.
Ya ce za’a fara horon nan ba da dadewa ba, kuma ya kare a watan Disamba na 2021, horon ya zama dole saboda yawancin ma’aikatan gwamnati da suka yi aiki na tsawon shekaru 20 zuwa 30 ba sa iya cin gajiyar kowane irin horo.
Ya ce tuni Gwamna Babagana Zulum ya aiwatar da mafi karancin albashi na N30,000, inda ya kara da cewa gwamnan ya samu rancen nera biliyan 12 daga Bankin Zenith, wanda aka yi amfani da shi wajen biyan alawus-alawus na tsoffin maaikatan gwamnati da suka yi ritaya a matakan jiha da na kananan hukumomi.
Ya kara da cewa ma’aikatan gwamnati za su shiga cikin fansho nan take idan sun yi ritaya daga aiki.

