Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewa Ruwan bama-bamai da jirgin yakin sojin Najeriya ya yi ya halaka Amir Buba Danfulani da wasu tsagerun kwamandojin ISWAP hudu a yankunan Tumbuns da Sambisa a arewa maso gabas.
PRNigeria ta tattaro cewa Amir Buba Danfulani ya kasance babban kwamandan ISWAP wanda ke aikin koyawa Fulani da makiyaya shiga kungiyar taaddanci.
Ya kuma jagoranci ayyukan yan taadda kama daga diban yan leken asiri da kuma masu karbar haraji. Rundunar sojojin Najeriya karkashin Operation HADIN KAI ce ta aiwatar da hare-haren a wurare daban-daban a cikin makon.
Wata majiyar sirri ta bayyana cewa, an girke jiragen Super Tucano, jirage masu saukar ungulu da sauran jiragen yaki a hare-haren na tsawon mako guda da aka gudanar a wurare daban-daban.
Majiyar ta ce kafin aiwatar da harin na musamman, binciken sirri ya gano sansanonin yan taadda a Tumbun Kaiyowa da Tumbun Allura wanda ke cike da ayyukan ISWAP da Boko Haram.
Ta kuma ce yan taadda na kuma amfani da sansanonin wajen harba makamai masu linzami a wuraren sojojin Najeriya da ke Mallam Fatori. Don haka sai rundunar Operation Hadin Kai ta tura jiragen yaki wanda ya yi raga-raga da yan taaddan domin hana su ci gaba da kaiwa sojoji hare-hare.

