Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar maya?an Boko Haram da ISWAP sun na?a sabbin kwamandoji tare da sanya sabon haraji ga manoma da ?an kasuwa da kuma masunta.
Jaridar PRNigeria ta ce maya?an sun yi sabbin na?e-na?en ne bayan kashe shugabannin ?ungiyoyin biyu da sojojin Najeriya suka yi.
Bayan mutuwar Abubakar Shekau da kumaha?ewar maya?an, kwamitin Al-Barnawiy ya sake dawo da Ba-Lawan don jagorantar abin da suka kira Daular Islama taAfrika, in ji jaridar.
Sannan maya?an za su dinga kar?ar N5,000 duk wata daga hannun ?an kasuwa da manoma, masunta kuma za su biya harajin N2,000 ga duk jakar kifi ?aya.
Maya?an Boko Haram da ISWAP ba su sha da da?i ba a ?an kwanakin nan, inda sojojin Najeriya ke ci gaba da fatattakarsu a sansanonin da suke ?uya.
A ranar Asabar rahotanni sun ce an kashe maya?an kusan 30 a jihar Yobe bayan harin kwatan ?auna da suka yi wa ayarin ?an sanda a kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.

