Site icon Muryar 'Yanci

Borno: An Na?a Sabon Shehun Dikwa

Gwamnatin jihar Borno ?ar?ashin jagorancin Gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum ta nada Abba Umar Jato a matsayin sabon Shehun Dikwa.

Abba Umar Jato ya gaji marigayi Shehu Mohammed Ibn Shehu Masta II El-Kanemi, wanda ya rasu a makon da ya gabata bayan fama da rashin lafiya.

Sanarwar na?in nashi na ?unshe ne a cikin wata takardar sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar aka rarraba ta ga manema labarai a birnin Maiduguri.

Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Usman Jidda Shuwa ne ya sanar da rasuwar Marigayi Shehu a garin Biu, jim kadan bayan gabatar da jawabi ga Sarkin Biu, Alhaji Mai Mustapha Umar Mustapha da Gwamna Babagana Umara Zulum ya yi a ranar Asabar da ta gabata.

An dauke shi zuwa Abuja kwana daya kafin rasuwarsa a ranar Juma’ar da ta gabata.

Wannan shi ne karo na uku da aka samu rasuwar manyan Sarakuna a Jihar Borno cikin kankanin lokaci, bayan na Shehun Bama da na Sarkin Biu a shekarar 2020.

Exit mobile version