Labarin dake shigo mana daga Jihar Neja na bayyana cewar Gwamnatin Jihar ta bayyana cewa Boko Haram sun kafa sansanoni a cikin ?ananan Hukumomin Shiroro da kuma Borgu da ke cikin Jihar.
Sai dai a wannan karon, Gwamnatin Jihar Neja ta ?ara fito da mummunan halin da ake ciki a yankunan, inda a cikin sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar, Ahmed Matane ya yi wa manema labarai ranar Talata a Minna, ya ce tuni har yan taadda sun fara bi cikin Masallatan Jumaa su na waazi a ?auyuka cewa jamaa su daina tura yayan su makarantun boko, kuma a kowa ya tashi ya bijire wa gwamnati.
Matane ya ce a halin da ake ciki, yan bindiga da yan samame sun ha?e kai su na ?o?arin ya?ar gwamnati a Shiroro, su na bi masallatan yankunan su na kafirta gwamnati da kuma hana yaya mata karatun boko.
Garuruwan da ISWAP/Boko Haram su ka bi su na waazin sun ha?a da Shuluba, Koki, Kusare da Madaka.
Sakataren Gwamnatin Tarayya ya ce yan ISWAP ?in har a cikin waazin su sukan ce, Duk wa?anda su ka bi mu za mu kare lafiya da rayukan kowa. Amma abin da mu ke so shi ne ku bi mu a bijire wa gwamnati.
Matane ya ce kuma su kan ce, Gwamnati ta sani mu ba masu garkuwa da mutane ba ne. Allah ne ya aiko mu domin mu kafa Daular Musulunci.
A cikin bayanin sa, Matane ya ?ara da cewa ISWAP na nan na ta ?o?arin kafa sansani a Gandun Dajin Babana da ke cikin ?aramar Hukumar Borgu.

