Site icon Muryar 'Yanci

Bauchi: ‘Yan Sanda Sun Gurfanar Da Masu Satar Mutane Da Mota

Kwamishinan Yan’sanda na Jihar Bauchi Sylvester Abiodun Alabi, ya ja hankalin iyaye kan yayansu, tare da gurfanar da wadanda suka shahara ta wajen garkuwa da mutane tare da satar motoci a cikin garin Bauchi da kewaye.

Kwamishinan da yake ma manema labarai bayanin nasarorin da hukumar ta samu na damke masu aikata laifuffuka dabam dabam a kokuwar cikin garin Bauchi.

Abiodun Alabi, Yace hukumar ta himmatu ne tare da samun bayanai daga sassan cikin garin tare da kai sumame a lungu da sako da jamianta suke kai wa lokaci zuwa lokaci don tsaron lafiya da dukiyan al’umma baki daya

Wadanda ake zargin dai sun hada da masu garkuwa da mutanen da karbar fansa, yara matasa da suka addabi mutane da satar babura musamman machinan yan achaba a fadar jihar.

Kana ya kara da cewa, akwai wadanda hukumar ta kamasu da laifin fashi da makami, tare da muggan makamai kamar su adduna, bindigogi Na ura Mai kwakwalwa (Computer) da akwatunan talabijin mai motsi da wasu kudade da aka bankado a cikin motar da ake zargi wadansu su biyu daga cikin wadanda aka gurfanar a gaban manema labarai.

Daga karshe kwamishinan Yan’sandan Abiodun Alabi, ya jaddada aniyar su na tsare dukiyoyin al’umma tare da bama jama’ar gari tabbacin samar da tsaro ko dare ko rana, Kuma yace suna yinnaikinsu Babu gidu babu ja baya donnganin annsaamr da tsaro mai inganci karkashin jagoranci sa a dukkan fadin jihar Bauchi.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Exit mobile version