Site icon Muryar 'Yanci

Bauchi: Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Sha Kaye A Zaben Fidda Gwani

Daga Adamu Shehu Bauchi

Jam’iyyar PDP a Jihar Bauchi ta gudanar da zabubukan ‘yan majalisun jiha dana tarayya, inda sakamakon zaben karamar hukumar Bauchi ya bar baya da kura, inda magoya bayan daya daga cikin ‘yan takarar kujerar, da ya sha kaye suka yi fatali da sakamakon, kuma shine mataimakin kakakin majalisar Jihar, Honorabul Danlami Kawule.

Tun a farko dai masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar sun yi kokarin fitar da ?an takarar ta hanyar daidaito amma batun ya ci tura, ba tare da ?ata lokaci ba aka shiga cikin za?en gadan-gadan

Daga karshe shugabannin gudanar da zaben na cikin gida suka bayyana Alhaji Aliyu Aminu Garu a matsayin wanda ya lashe zaben da gagarumin rinjaye, bayan deliget sun kada kuri’unsu aka kirga a karshe

Masu kada kuri’ar dai tun a farko aka tantance su 37 inda Ali Garu ya lashe da kuriu masu yawa kimanin 27 sai Mai biye mashi mataimakin Shugaban majalisa Danlami Kawule ya tashi da kuri’u goma 10 kana dayan Malam Yahuza Bauchi bai samu kuri’a ko guda ?aya ba

Dan takarar da ya lashe za?en ya gode wa Allah da ya bashi wannan nasara, kana yace wadanda suka fadi su zo su hada kai domin su ci babban zabe na gama gari dake tafe a 2023.

Exit mobile version